1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da kai hare-hare a Siriya

July 28, 2012

Sojojin Siriya sun kai sabbin hare-hare da jiragen sama a garin Allep inda fada ya barke

https://p.dw.com/p/15g1T
In this Friday, July 27, 2012 photo, armed Syrian rebels stand beside a destroyed Syrian army armored vehicle in Homs, Syria. It has been a difficult two weeks for the Syrian government with rebel assaults first on the capital, Damascus, and then on Aleppo, as well as several high-profile defections and a bomb that killed four top security officials. (AP Photo/Fadi Zaidan)
Hoto: dapd

Dakarun gwamnatin Siriya sun ƙaddamar da hare-haren da ake sa ran zasu kai birnin Alepp tun a 'yan kwanakin da suka gabata. Bisa bayanan da 'yan adawa suka bayar, dakarun sojin sun fara amfani da jiragen yaƙi masu saukar ungulu wajen kai hari kan dakarun tawayen.

Abunda ke tilastwa 'yan adawan ficcewa daga yankunan da suke jagoranta a cikin birnin.

Faɗan dai ya yi tsanani sosai a Alepp tun da aka fara wannan borai a cewar masu sanya ido daga wata ƙungiyar kare haƙƙin bil adama da ke da Shelkwatarta a birnin London. A dai bangare hukumomin Rasha sun ce basu da wata yarjejeniyar baiwa shugaba Assad mafuka,kuma basu ma taba tunanin haka ba iinji ministan harakokin wajen Rasha Sergei Lavrov wanda ya karyata jita-jitan da a ke bazawa na cewar Shugaban zai karbi mafuka daga kasar ta Rasha.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Yahouza Sadissou Madobi