1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da gwabza ƙazamin faɗa a yankuna da dama na Libiya

March 5, 2011

Mutane da dama aka kashe a faɗan baya bayan nan tsakanin dakarun 'yan tawaye da masu biyayya ga shugaba Muammar Gaddafi.

https://p.dw.com/p/10U04
'Yan tawaye da suka yi galaba kan dakarun GaddafiHoto: AP

'Yan tawaye a Libiya sun yi iƙirarin sake ƙwace birnin Zawiyah dake yammacin ƙasar daga hannu dakarun dake biyayya da shugaba Muammar Gaddafi. To sai dai an rawaito cewa dakarun Gaddafi sun kutsa cikin wasu yankuna na yammacin ƙasar. Aƙalla mutane 50 aka kashe a faɗan baya bayan nan. 'Yan tawayen sun kuma ce sun ƙwace garin Ras Lanuf mai matatun man fetir dake gaɓar tekun gabacin ƙasar. A kuma can kusa da Bengazi birni na biyu mafi girma da shi ma yake a gabacin ƙasar ta Libiya aƙalla mutane 19 suka rasu a fashewar wasu ababa a wani wurin ajiye makamai.

A dangane da mawuyacin hali da kuma hare hare da sojoji ke kaiwa, yawan 'yan gudun hijira dake ƙoƙarin ficewa daga Libiya ya ragu. Mai magana da yawun Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce dubban baƙi 'yan ci rani na ƙin fita waje saboda fargaba game da rayuwarsu. Ta ce Majalisar za ta gudanar da bincike akan rahotannin da ke cewa dakarun Muammar Gaddafi na hana 'yan gudun hijira tsallake kan iyakokin ƙasar.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman