1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A Ingila Tottenham ta lallasa Chelsea da ci biyu

Lateefa Mustapha Ja'afar SB/MAB
February 27, 2023

Har yanzu dai Bayern Munich ke saman tebur da maki 46 kana Borussia Dortmund ke biye mata a wasannin lig na Jamus.

https://p.dw.com/p/4O2Kx
Saudi Arabien Spanischer Super Cup Barcelona
'Yan wasan kungiyar Barcelona ta SpainHoto: Giuseppe Cacace/AFP/Getty Images

Akwai yiwuwar shahararren dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafar Barcelona ta Spain Robert Lewandowski ba zai iya buga wasan kusa da na karshe wato semi-final, a gasar lashe kofin kalubale na Spain din wato Copa del Rey. Kungiyar ta Barcelona dai, za ta fafta ne da babbar abokiyar hmyyarta Real Madrid a filin wasa na Santiago Bernabeu a Alhamis din wannan mkon.

Fussball Champions League Robert Lewandowski FC Barcelona, Barca 09
Robert Lewandowski na kungiyar BarcelonaHoto: IMAGO/MIS

Rahotanni sun nunar da cewa Lewandowski da ya fi kowa zira kwallo a kungiyar tasa, ya gurde ne a idon sawu. A baya-bayan nan dai Barcelona na shan kashi a wasanninta da ta buga, inda Manchester United ta fatattake su daga gasar zakarun Turai Europa League yayin da a gida kuma Almeria ta lallasata a gasar La Liga ta kasar Spaniyan.

A nan gida Jamus kuma, FSV Mainz 05 ta lallasa Borussia Mönchengladbach da ci hudu da nema yayin da TSG 1899 Hoffenheim ta sha kashi a gida da ci daya mai ban haushi a hannun Borussia Dortmund.

Bundesliga Fussball 1. FC Koeln vs VfL Wolfsburg
Kungiyar FC CologneHoto: Ralf Treese/IMAGO

Ita ma dai  Cologne ta sha kashi a gida da ci biyu da neman a hannun Wolfsburg, kana Werder Bremen ta caskara VfL Bochum da ci uku da nema. Ita ma dai Hertha Berlin ta samu nasara a kan Augsburg da ci biyu da nema, kana RB Leipzig ta samu galaba a kan Eintracht Frankfurt da ci biyu da nema. Ita ma dai Schalke 04 ta yi abin kai, inda ta lallasa Stuttgart da ci biyu da daya, yayin da aka tashi wasa kunnen doki daya da daya tsakanin Freiburg da Bayer Leverkusen. Bayern Munich kuwa, ta samu nasara ne a kan Union Berlin da ke mata barazanar nasara a bana da ci uku da nema. Har yanzu dai Bayern Munich ke saman tebur da maki 46 kana Borussia Dortmund ke biye mata ita ma da maki 46 yayin da Union Berlin ke matsayi na uku da maki 43.

Tottenham Hotspur - Eintracht Frankfurt
Kungiyar TottenhamHoto: HMB Media/picture alliance

A gasar Premier League ta Ingila kuwa, Tottenham ta lallasa Chelsea da ci biyu da nema, kana Arsenal ta bi Leicester City har gida ta kuma lallasa ta da ci daya mai ban haushi. Ita kuwa West Ham United ta yi wa kungiyar kwallon kafa ta Nottingham Forest cin kaca hudu da nema, yayin da aka tashi wasa canjaras babu ci tsakanin Crystal Palace da FC Liverpool. Har yanzu dai Arsenal ke saman tebur da maki 57, kana Manchester City ke biye mata da maki 55 sai kuma Manchester United a matsayi na uku da maki 49.

Shahararren dan wasan kwallon Tennis din nan Novak Djokovic ya zamo mafi shahara a duniya a bangaren maza da mata baki daya. Djokovic ya samu wannan nasarar ne, bayan da ya yi nasarar zama a matakin farko a jadawalin 'yan wasan Tennis na duniya har na tsawon makonni 378.

Tennis | Australian Open Finale | Gewinner Novak Djokovic
Novak Djokovic dan wasan tennisHoto: Paul Crock/AFP

Dan kasar Sabiyan dai ya karya kofin fitacciyar 'yar wasan Tennis din nan ta Jamus Stefanie Graf da ta kwashe makonni 377 a matsayin zakakurar 'yar wasan Tennis din a bangaren mata. A hannu guda kuma fitaccen dan wasan Tennis din nan da ya yi nasarar zama zakaran bababbar gasar Tennis din nan ta Grand Slam, wato Andy Murray ya bayyana janyewarsa daga gasar Tennis da za a gudanar a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa. Mai shekaru 35 a duniya, Murray dai ya bayyana janyewar tasa ne sakamakon ciwon kugu. Da ma dai ba sabon abu bane matsalar ta ciwon kugu ga Murray kasancewar koda a 2019, sai da ya kusan bayyana yin ritaya sakamakon ciwon kugun da har sai da aka yi masa tiyata.