1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan na ci gaba da zama cikin tashin hankali

Abdourahamane Hassane SB
April 27, 2023

Yarjejeniyar tsaigata bude wuta a Sudan na kwnaki uku wacce gwamnatin Amirka ta taimaka aka kulla ta gaza saboda bangarorin biyu ba su mutunta yarjejeniyar ba abin da ya sa ake ci gaba da yin tashin hankalin.

https://p.dw.com/p/4QaDy
Sudan | Birnin Khartum na kasar Sudan lokacin tsagaita wuta
Birnin Khartum na kasar Sudan lokacin tsagaita wutaHoto: AA/picture alliance

A birnin Khartum an ci gaba da gwabza kazamin fada a wurare mafi mahimmanci tsakanin dakarun gwamnatin da na rundunar RSF.

Dakarun sa-kai na Janar Mohamed Hamdane Daglo wadanda ke adawa da gwamnatin Janar Abdel Fattah al-Burhane, da ke kan madafun iko tun bayan juyin mulkin da aka yi a watan Oktoban 2021. sun ce sun kwace iko da wata matatar mai da tashar wutar lantarki mai nisan kilomita 70 daga arewacin Khartum.

Karin Bayani: Halin tsaka mai wuya a rikicin kasar Sudan

Sudan | Birnin Khartum na kasar Sudan lokacin tsagaita wuta
Birnin Khartum na kasar Sudan lokacin tsagaita wutaHoto: Ahmed Satti/AA/picture alliance

A kan iyakar Chadi ana fafatawa kuma ana samun rahotanni masu tayar da hankali game da kabilun da ke dauke da makamai domin shiga yakin na Sudan. Shaidu gani da ido sun ce arangama tsakanin sojoji gwamnatin da na rundunar RSF da jiragen sama na yaki, ta kaure  a Wad Banda, a kudancin Kordofan yankin da ke kan iyaka da Darfur.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce ta damu a game da wani hadarin da ka iya faruwa bayan da rundunar RSF ta kame dakin gwaje-gwajen na kiwon lafiya a Khartum, wanda jamian kiwon lafiya da ke kula da yaki da cututtukan da kyanda, da kwalara da kuma polio suke yin aiki a ciki.

Sudan | Tsohon Shugaba Omar al-Bashir
Omar al-Bashir tsohon shugaban kasar SudanHoto: Mohamed Khidir/Xinhua/Imago

A cewar lauyoyin, fursunonin siyasa da ke tsare tare da tsohon shugasban kasar Omar al-Bashir,da yawa sun tsere daga gidan kurkukun Kober inda ake tsare da su. Ahmed Harun daya daga cikin na kusa da al Bashir wanda kotun ICC ke neman ruwa jalo ya tabbatar da cewar ya arce daga gidan kurkukun tare da wasu fursunonin.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce karancin abinci, da ruwan sha, da magunguna da kuma man fetur na kara yin muni, musamman a birnin Khartum da kewaye.

A cewar Majalisar ana sa ran mata dubu 24 za su haihu  a cikin makonni masu zuwa, wadanda zasu fuskanci matsala mai tsanani wajen samun kulawa yayin da a cewar kungiyar likitocin, kusan kashi uku cikin hudu na asibitoci ba su da aiki. Kimanin mutane dubu 270,000 suka tsere zuwa makwabciyarta Chadi da Sudan ta Kudu sakamakion fada da kawo yanzu mutane sama da 400 suka mutu kana wasu dubu hudu suka jikkata. Yanzu haka kuma kasashen duniya na ci gaba da kwashe 'yan kasahensu. Tuni dai Faransa da Saudiyya da Chaina da Amirka da wasu sauran kasashen Afirka suka kwashe jama'arsu daga kasar ta Sudan.