1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ɗage gudanar da zaɓen gwamnoni a jihohin Kaduna da Bauchi da kwanaki biyu-INEC

April 21, 2011

Ƙungiyoyin al'uma da na addinai na ci-gaba da yin kira da a kwantar da hankula da nuna ya kamata bayan rikicin zaɓen shugaban ƙasa.

https://p.dw.com/p/112BS
Farfesa Attahiru Jega shugaban INEC a NajeriyaHoto: AP

Shugaba Najeriya Goodluck Jonathan ya ce za a gudanar da zaɓen gwamnonin jihohin ƙasar kamar yadda aka shirya duk kuwa da tashen tashen hankulan da aka fuskanta a sassa daban daban na arewacin ƙasar bayan zaɓen shugaban ƙasa. A cikin wani jawabi da yayi shugaba Jonathan ya ce ana ci-gaba da ƙokarin maido da doka da oda da kwanciyar hankali a ƙasar, wadda ta fi kowace yawan al'uma a nahiyar Afirka. A ranar Talata mai zuwa ne za a yi zaɓen gwamnoni da na wakilan majalisun dokokin jihohin ƙasar ta Najeriya. To sai dai hukumar azɓen ƙasar mai zaman kanta ta ce ta ɗage gudanar da zaɓen a jihohin Kaduna da Bauchi ta kwanaki biyu wato zuwa ranar Alhamis, saboda rashin cikakken tsaro a jihohin.

Tuni dai ƙungiyoyin addinai da shugabannin al'uma ke yin kira da a kwantar da hankula kana a tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin jama'a. An yi kuma kira ga jama'a da su fita kaɗa ƙuri'a a lokacin zaɓukan na gwamnoni.

A ƙasa mun yi muku tanadin sautin rahotanni daban daban game da halin da ake ciki a Najeriya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Ahmad Tijani Lawal