1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya na cin zafin jama'a

Usman Shehu Usman
February 6, 2020

Kungiyar kare hakkin jama'a ta kasa da kasa Amnesty International, ta zargi hukumomin Saudiyya da cin zarfin jama'a cikin sirri daga ciki har da malaman addini da basa bin ra'ayin gwamnati

https://p.dw.com/p/3XM5H
London Mohammed bin Salman
Hoto: picture-alliance/empics/V. Jones

Kungiyar ta ce Saudiyya ta kafa wata kotu ta musamman don hukunta wadanda ke aikata man'yan lafuka, amma kuma ana labewa da kotun ana cin zarafin mutanen da ke adawa da gwamnati, ciki har da shehunan malaman Saudiyya wadanda ba sa bin ra'ayin gwamnatin Riyard. Amnesty International ta ce akasarin karakin da ake wa wannan kotu ta musamman, ana tsare wadanda ake kai kara a kurkuku, kana ana hana musu damar yin magana da lawya kuma ko iyalai da dangi basa iya ziyartan wadda aka tsare. Kungiyar ta kara da cewa akasarin hukuncin kotun ba a daukar dogon lokaci, kana akan ba da hujja ne da shaidar wanda ya aikata laifi, a kalaman da ya furta bayan shan azabar jami'an tsaro. Tun a shekara ta 2008 ne dai aka kafa wannan kotu ta musamman a kasar ta Saudiyya.