1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya ta fidda rahoto a kan Yemen

Zulaiha Abubakar MNA
August 29, 2018

Hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta fidda wani rahoton da ya bayyana gwamnatin Yemen da kasashen Daular Larabawa da kuma kasar Saudiyya a matsayin kasashen da ke aikata laifukan yaki a Yemen.

https://p.dw.com/p/33vEh
Lokacin jana'izar yara kanana da wani harin sojojin kawance ya hallaka a Yemen
Lokacin jana'izar yara kanana da wani harin sojojin kawance ya hallaka a YemenHoto: Reuters/N. Rahma

Rahoton irinsa na farko tun bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta umarci hukumar ta gabatar da bincike a kan fyade da tirsasa yara kanana shiga aikin soja da tsare al'ummar kasar ta Yemen a gidajen yari da kuma gana wa mutane azaba da ya zama ruwan dare tun bayan barkewar rikici a kasar, ya janyo wa kasar Saudiyya matsin lamba daga kasashen duniya da kuma kungiyoyin kare hakkin dan Adam.

Tun bayan da 'yan tawayen Houthi suka hambarar da gwamnatin Yemen a shekara ta 2015 Saudiyya ta dauki alwashin ganin bayan 'yan tawayen na Houthi lamarin da ke ci gaba da janyo asarar rayukan fararen hula.

Da yake mayar da martani a kan wannan zargi jakadan kasar Saudiyya a Yemen ya ce wannan batu ne marar tushe.

Hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya dai ta bayyana gwamnatin Yemen da kasashen Daular Larabawa da kuma kasar Saudiyya a matsayin kasashen da ke aikata laifukan yaki a kasar Yemen.