1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi ƙasar Burma da cin zarafin al´umma

Ibrahim SaniDecember 8, 2007
https://p.dw.com/p/CZ2Z

Hukumar kare haƙƙin bil adama ta Human Rights Watch ta zargi Gwamnatin Burma da take hakkoki na bil adama a ƙasar. A wani rahoto da hukumar ta fitar mai shafi 140, ta zargi mahukuntan ƙasar da gallazawa ´Yan adawa tare da sanadin rayukan da yawa daga cikinsu. Hakan a cewar hukumar ta Human Rights Watch ya auku ne, a lokacin zanga-zangar adawa da Gwamnatin ƙasar ´Yan makonni kaɗan da su ka gabata. Ƙasar Burma a cewar Human Rights Watch na buƙatar yin canje-canje a yanayi na tafiyar da harkokin mulki a ƙasar. Bisa hakan Hukumar ta ƙasa da ƙasa ta buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya matsawa ƙasar lamba, don ganin burin da aka sa a gaba an cin ma sa. A waje daya kuma Hukumar ta Human Rights Watch ta kuma zargi ƙasashen Sin da Russia da Indiya da kuma Thailand, da gaza shawo kan badaƙalar siyasa da ƙasar take fuskanta. Ƙasashen a cewar Hukumar nada kyakkyawar rawa da za su iya takawa wajen shawo rikicin siyasar ƙasar, kasancewar dangantakar dake tsakanin su da ƙasar ta Burma.