1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi wa mutane miliyan 20 rigakafin corona a Birtaniya

Ahmed Salisu
February 27, 2021

Adadin jama'ar da aka yi wa zagayen farko na rigakafin annobar coronavirus a Birtaniya yanzu haka ya tasamma miliyan 20.

https://p.dw.com/p/3q10q
Großbritannien London | Coronavirus | Impfung Pfizer/BioNTech
Hoto: Victoria Jones/REUTERS

Hukumomi na kiwon lafiya a kasar ne suka fidda wadannan alkaluma a wannan Asabar din, inda suka ce suna ci gaba da bakin kokarinsu wajen ganin an ci gaba da yin rigakafin ta yadda gaba dayan al'ummar kasar za su samu.

Birtaniya dai na daga cikin kasashen Turai da annobar ta yi wa ta'annati kuma har yanzu ake ci gaba da samun wadanda ke kamuwa da cutar da ma wadanda ke rasa rayukansu sakamakon kamuwa da ita, sai dai adadin da ake samu a yanzu bai kai wanda aka rika gani a watannin da suka gabata ba.