1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi tir da Rasha da China a taron aminan Siriya

July 6, 2012

Taron na birnin Paris ya zo ne a daidai lokacin da ɗaya daga cikin manyan janar janar ɗin soji na shugaba Bashar al-Assad ya canza sheƙa.

https://p.dw.com/p/15T8v
French President Francois Hollande delivers his speech at the "Friends of Syria" conference in Paris, Friday, July 6, 2012. Syrian opposition leaders are pressing diplomats at an international conference for a no-fly zone over Syria, but the U.S. and its European and Arab partners are expected to focus on economic sanctions instead. (Foto:Jacques Brinon, Pool/AP/dapd)
Hoto: dapd

Taron ƙasashen duniya a kan ƙasar Siriya ya yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ta yi amfani da barazanar takunkumai domin matsa lambar kawo canji a Siriya.

Wakila daga ƙasashe fiye da 100 dake kiran kansu wai aminan Siriya sun ƙuduri aniyar ɗaukan matakai cikin gaggawa domin hana ɓarkewar yaƙin basasa a Siriya. Tun a jawabinsa na buɗe taron a birnin Paris, shugaban Faransa Francois Hollande ya yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya ta ja kunnen gwamnatin Bashar al-Assad fiye da a baya.

"Wannan rikicin ka iya rikiɗewa zuwa wani yaƙin basasa gadan gadan, dalilin da ya sa kenan ya zama wajibi mu dakatar da wannan rikici. Hakan yana da muhimmanci ga siyasa da kuma jin ƙan jama'a. Dole mu taimaka wa al'umar Siriya, dole ne Assad ya sauka."

Mai masaukin baƙin ya ce rabin yawan ƙasashen duniya suka samu wakilci a taron dake da burin wanzar da zaman lafiya a Siriya. To sai dai ina amfanin rabin yawan ƙasashen duniya, idan manyan ƙasashe biyu masu muhimmanci ga duniyar wato Rasha da China ba su halarci taron ba? A saboda haka ne sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta yi amfani da taron wajen sukar lamirin ƙasashen biyu da zama karan tsaye ga duk ƙoƙarin warware rikicin.

French President Francois Hollande delivers his speech at the "Friends of Syria" conference in Paris, Friday July 6, 2012. Syrian opposition leaders are pressing diplomats at an international conference for a no-fly zone over Syria, but the U.S. and its European and Arab partners are expected to focus on economic sanctions instead. (Foto:Jacques Brinon, Pool/AP/dapd)
Hoto: dapd

"Me ƙasashen da kuma ƙungiyoyin da suka samu wakilici a wannan taron za su iya yi? Ina kira gareku da ku fuskanci Rasha da China, ba kawai kira gare su za ku yi ba, a'a ku kuma buƙace su da su kau daga bayan fage su zo su fara goyon bayan abin da al'umar Siriya ke so."

Muhimmancin ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya

Sakatariyar ta harkokin wajen Amirka ta kuma nuna buƙatar zartas da wani kudurin Majalisar Ɗinkin Duniya a kan wata gwamnatin riƙon ƙwarya a Siriya, inda ta ce yana da muhimmanci a sake waiwayar kwamitin sulhu domin aiwatar da yarjejeniyar birnin Geneva.

Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle, wanda ya wakilci ƙasarsa a taron na aminan Siriya, ya nuna goyon bayan kiran da aka yi na amfani da hanyoyin lumana wajen warware rikicin.

Secretary of State Hillary Rodham Clinton, right, and German Foreign Minister Guido Westerwelle listen during the "Friends of Syria" conference in Paris, Friday, July 6, 2012. Syrian opposition leaders are pressing diplomats at an international conference for a no-fly zone over Syria, but the U.S. and its European and Arab partners are expected to focus on economic sanctions instead. (Foto:Jacques Brinon, Pool/AP/dapd)
Hoto: dapd

"Za mu ƙara matsa wa gwamnatin Assad lamba a dukkan ɓangarorin siyasa, tattalin arziki da kuɗi, kuma muna roƙo ga kowa da kowa da su shiga a cikin takunkuman da za su mayar da gwamnatin Assad saniyar ware."

Bambamcin ra'ayin kan shirin Kofi Annan

'Yan awadar Siriya da ƙasashen yamma da kuma Rasha sun ba wa shirin samar da zaman lafiya da manzon ƙasashen duniya a Siriya Kofi Annan ya tsara wanda ya tanadi kafa gwamnatin wucin gadi, fassara dabam dabam, amma Hillary Clinton ta ce shirin na kira ga Assad da ya sauka.

A martanin farko da suka mayar 'yan adawar Siriya sun nuna takaicinsu ga sakamakon taron suna masu cewa sun gaji da gafara sa har yanzu ba su ƙaho ba.

A wannan Juma'a gwamnatin Assad ta fuskanci sabon koma-baya lokacin da janar Munaf Tlass, ɗan tsohon ministan tsaron Siriya kuma na kurkusa da mahaifin Assad, wato Hafez, ya canza sheƙa. Tlass memba a majalisar zartaswar Siriya kuma abokin Assad tun suna yara, shi ne jami'in soja mafi girman muƙami da ya juya wa gwamnati baya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman