1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

301211 NGOs Ägypten

December 30, 2011

Ƙasashen Jamus da Amirka da ƙungiyoyin kare haƙin Bil Adama sun nuna matuƙar damuwa ga samamen da hukumomin tsaron Masar suka kai kan ƙungiyoyi masu zaman kansu.

https://p.dw.com/p/13c4R
Egyptian military stand guard as officials raid one of the non-governmental organization offices in Cairo, Egypt, Thursday, Dec. 29, 2011. Egyptian soldiers and police stormed non-governmental organization offices throughout the country on Thursday, banning employees inside from leaving while they interrogated them and searched through computer files, an activist and security official said. (Foto:Mohammed Asad/AP/dapd)
Hoto: dapd

Hukumomin Masar dai na zargin waɗannan ƙungiyoyi da suka haɗa da na gida da na waje, da karɓar kuɗaɗen haramun daga ƙetare, sannan suna gudanar da aiki ba da izini ba.

Julie Hughes ta cibiyar demokraɗiyya ta ƙasa ta kaɗu lokacin da jami'an tsaro da jami'an hukumar gabatar da ƙara ta Masar suka buƙaci da a ba su wasu fail-fail da damar ganin abubuwan dake cikin na'urorin komfuta na cibiyar.

Ƙungiyar tana taimakawa da girke demokraɗiyya a ƙasashe 65. Tun shekaru shida da suka wuce muke aiki a Masar, kuma tun bayan mana rajista a shekarar 2005, muke aiki tsakani da Allah a cikin ƙasar. Ganin wannan abun ya faru a wannan lokaci na shirye-shiryen kafa demoƙardiyya a ƙasar, babban abin damuwa ne garemu."

Cibiyar mai samun tallafin gwamnatin Amirka kuma ke da alaƙa da 'yan Democrat na Amirka, na daga cikin ƙungiyoyi masu zaman kansu 17 da aka kaiwa samame a ranar Alhamis. Cikinsu har da gidauniyar Konrad-Adenauer ta kurkusa da jam'iyar CDU a Jamus da ƙarin wasu ƙungiyoyin Amirka guda biyu waɗanda dukkansu aka ƙwace kamfutocinsu da sauran takardun aiki, sannan an tsare ma'aikatansu a ciki ofis an yi musu tambayoyi.

Mahukuntan Masar sun ce dalilin wannan samame shi ne zargin da ake wa ƙungiyoyin da karɓar kuɗaɗen tallafi daga ƙetare ba bisa ƙa'ida ba. Tun a watannin baya hukumomin Masar sun binciki kafofin samun tallafi na wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu, musamman ƙungiyoyin kare hakin bil Adama, abin da ya sanya Heba Morayef ta ƙungiyar Human Rights Watch zargin cewa wannan matakin na da nasaba da siyasa.

Workers from a non-governmental organization National Democratic Institute, or NDI, wait as Egyptian officials raid their office in Cairo, Egypt, Thursday, Dec. 29, 2011. Egyptian soldiers and police stormed non-governmental organization offices throughout the country on Thursday, banning employees inside from leaving while they interrogated them and searched through computer files, an activist and security official said. (Foto:Mohammed Asad/AP/dapd)
Hoto: dapd

"Matsalar dake akwai a nan ita ce dokar aikin ƙungiyoyi masu zaman kansu tana da tsauri, kuma ba mu ga wani sauyin daidai da ta kungiyoyin ƙwadago da jam'iyun siyasa ba. Wani yunƙuri ne na rufe bakin jama'a musamman ƙungiyoyin kare haƙin bil Adama, waɗanda suka fi ɗaga murya kuma suke tir da matakan ƙarfi da sojoji ke ɗauka a watannin bayan nan."

A halin da ake ciki ƙasashen duniya ciki har da Jamus da Amirka sun yi tir da samamen, inda tuni gwamnati a Berlin ta gaiyaci jakadan Masar a Jamus da ya je yayi mata bayani game da samame. Ita kuwa gwamnatin Amirka a ta bakin mai magana da yawon ma'aikatar waje Victoria Nuland cewa ta yi:

"Muna kira ga gwamnatin Masar da ta hanzarta kawo ƙarshen cin mutuncin kungiyoyi masu zaman kansu da ma'aikantansu, ta mayar musu da kayan aikinsu kana ta warware wannan batu nan-take."

Su ma masu fafatukar girke demokraɗiyya a Masar sun yi suka ga matakin suna masu zargin shugabannin gwamnatin mulkin soji da fara wata yekuwa ta tursasa wa duk wani ɗan adawa dake samun tallafi daga ƙetare.

Mawallafa: Hans Michael Ehl / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Ahmad Tijani Lawal