1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mahara sun halaka mutane a Nijar

August 17, 2021

A Jamhuriyar Nijar mahara sun hallaka mutane 37 a yankin yammacin kasar da ke fama da matsalar tsaro. Wani jami'i a yankin ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP a wannan Talata.

https://p.dw.com/p/3z5UI
Deutschland l Besuch des Nigerianischen Präsidenten in Berlin
Hoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

Jami'in ya ce a ranar Litinin ce maharan suka isa kauyen Darey-Daye da ke yankin Tillaberi a kan babura a daidai lokacin mutanen yankin ke ayyukansu na yau da kullum. Rahotanni sun ce cikin mutane 37 da 'yan bindigar suka hallaka akwai mata guda hudu da kananan yara 13.

Kisan mutanen a yankin Tillaberi shi ne na biyar mafi muni a cikin 'yan watannin nan, inda a yanzu wasu ke hasashen mahara sun hallaka kimanin mutane 450 a cikin wannan shekarar.