1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwamitin Sulhu ya nemi a kawo karshen fadan Habasha

Ramatu Garba Baba
November 6, 2021

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kara yin kira da babban murya ga masu fada da juna a Habasha da su tsagaita bude wuta saboda halin da fararen hula ke ciki na kuncin rayuwa.

https://p.dw.com/p/42g1M
UN I Krise in Tigray
Hoto: AP/picture alliance

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya sake yin kira da babban murya kan kawo karshen rikicin kasar Habasha da ya ce ya jefa fararen hula cikin tsanani ba tare da samun damar isar musu da agaji ba. Kwamitin ya kara baiyana fargaba kan illolin da rikicin zai haifar ga tsaron kasashen da ke makwabtaka da Habashan inda ya nemi bangarorin biyu da su kawo karshen musayar munanan kalaman da ke rura wutar rikicin.

Sanarwar da kwamitin ya fitar da aka kuma gabatar ma manema labarai, na dauke da saka hannun kasashe akalla goma sha biyar mambobin kwamitin.

A dai ranar Alhamis da ta gabata aka cika shekara guda cur da barkewar rikicin da ya rikide zuwa yakin basasa. Dubbai sun rasa rayukansu wasu miliyoyi sun rikide zuwa 'yan gudun hijira a sakamakon tashin hankali a tsakanin bangaren gwamnati da mayakan kungiyar kwatar 'yancin kan yankin Tigray.