1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi girgizar kasa mai karfin 6.3 a Girka

Mouhamadou Awal Balarabe
October 12, 2021

An yi girgizar kasa mai karfin maki 6.3 a ma'aunin Richter a tsibirin Crete da ke kudancin Girka ba tare da haddasa asarar rayuka ba, kamar yadda kafofin yada labarai na cikin gida suka ruwaito.

https://p.dw.com/p/41a7N
Griechenland | Erdbeben Kreta
Hoto: Harry Nakos/AP Photo/picture alliance

Kafofin yada labarai na Girka sun ce, an ji karfin girgizar kasar har i zuwa wasu tsibirai da kuma Tekun Aegean, nesa da yankunan da mutane ke zaune. Wannan iftila'in ya zo makonni biyu bayan girgizar kasa mai karfi maki 5.8 a ma'aunin Richter a Girka, wacce ta yi sanadin mutuwar mutum daya, ta raunata goma kuma ta haifar da gagarumar barna musamman a kauyen Arkalohori.

Ita dai kasar Girka ta saba fuskantar iftila'in girgizar kasa a tarihinta. Ko a ranar 3 ga Maris na wannan shekarar, sai da girgizar kasa ta yi sanadiyyar mutuwar mutum daya tare da raunata goma da kuma barnata dukiya mai yawa.  A ranar 30 ga watan Oktoba 2020 ma dai, girgizar kasa mai karfin maki 7 a ma'aunin Richter ta afku a tekun Aegean tsakanin tsibirin Samos na Girka da garin Izmir na Turkiyya, inda ta kashe mutanen 114 a Turkiyya da kuma biyu a Samo.