1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an tsaron sa kai a Maiduguri sun sallami yara kanana

Zulaiha Abubakar
October 12, 2018

Hunkumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta yaba wa Jami'an tsaron sa kai a Maiduguri bisa sallamar yara 830 wadanda suka sadaukar da kansu don yaki da Boko Haram a yankin.

https://p.dw.com/p/36Rbj
Nigeria Traditionelle Jäger Anti Boko Haram Kämpfer
Hoto: Reuters/Joe Penney

Wannan dai shi ne karo na farko da rundunar tsaron sa kan ta fara sallamar yara tun bayan da kungiyar ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar daina daukar yara kanana a matsayin jami'an tsaron sa kai a sheakara ta 2017,wani bincike da hukumar kula da yara kananan ta gudanar ya gano yaran da yawan su ya kai 1469 ciki kuwa har da 'yan mata da yawan su ya kai 294 a matsayin jami'an tsaron sa kai a Maiduguri.