1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tafka muhawarar kashe kafin babban zaben Jamus

February 20, 2025

Kafofin watsa labaran cikin gida a Jamus, sun watsa muhawarar da aka tafka a tsakanin shugaban gwamnatin kasar Olaf Scholz da abokin hamayyarsa na masu ra'ayin rikau, Friedrich Merz.

https://p.dw.com/p/4ql6N
Olaf Scholz tare da Friedrich Merz
Olaf Scholz da Friedrich MerzHoto: Michael Kappeler/dpa-Pool/dpa/picture alliance

Cikin daren da ya gabata ne dai aka watsa muhawarar a karo na biyu, kuma dukkanin 'yan siyasar sun maida hankali ne a kan tsari na walwalar jama'a musamman sauyi a yanayin rayuwa da batun shige-da-fice na baki.

Haka nan manyan 'yan siyasar Jamus din sun yi bayanai game da tattalin arziki da ke tangal-tangal, inda Olaf Scholz ya karfafa kalamai a kan haraji yayin da Friedrich Merz ya bukaci a sassauta tsananin tsare-tsaren gwamnati.

Yayin dai da ya rage kwanaki uku a yi zaben Jamus, jam'iyyar Merz ta CDU/CSU ce ke kan gaba a kuri'ar jin ra'ayin jama'a, yayin da jam'iyyar AfD ta masu tsananin kishin kasa ke biye mata.

Shi kuwa Olaf Scholz na SPD na matsayi nauku ne kamar yadda ra'ayoyin ke nunawa.

Akalla dai mutum miliyan 59 ne za su kada kuri'a a ranar Lahadin da ke tafe 23 ga wannan wata na Fabrairu.