1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kawo karshen yaki a Habasha

Hanna Demisse, SB
December 12, 2022

Bayan shafe shekaru biyu cikin yakin basasa a kasar Habasha tsakanin dakarun gwamnati da mayakan yankin Tigray a karshe an saka hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Nuwamba da ya gabata.

https://p.dw.com/p/4Kq2c
Wakilin gwamnati  Redwan Hussien  da wakilin 'yan tawaye Tigray Getachew Reda sun saka hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya
Wakilin gwamnati  Redwan Hussien da wakilin 'yan tawaye Tigray Getachew Reda sun saka hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiyaHoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Kawo yanzu an tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu, abin da ke nuna alamun kawo karshen yakin basasan na shekaru biyu da ya janyo salwantar rayuka da dama. Masu sharhi kan harkokin yau da kullum na ganin tsagaita wutar na da tasiri kan samun zaman lafiya musamman a yankunan da aka samu tashe-tashen hankula na Tigray da Amhara gami da Afar. Dr. Taye Negussie mai binciken harkokin siyasa a jami'ar birnin Addis Ababa ya ce duk bangarorin sai sun ci gaba da nuna sanin yakamata: "Harkokin rayuwa da na kasuwanci da ake yi a baya ake bukatar mayar da su. Ba za manta da abin da ya faru ba, za a koyi yafewa domin rayuwa tare. Yana da kyau sasantawa ta siyasa a matakin kasa, kamar yadda ake maganar yafewa juna. Ba za a iya mantawa da abin da ya faru ba, amma za a ci gaba da rayuwa da mu'ammala kan harkokin rayuwa da kasuwanci. Akwai abubuwan da za su iya zagon kasa kan tattaunawar zaman lafiya. A hannu daya akwai kasashe ketere da kafofin sada zumunta kana babu wani binciken da aka yi na sanin wadanda suka aikata ta'asa daga duk bangarorin.

Gwamnatin Habasha na neman taimakon jama'a domin kara samar da zaman lafiya

Pretoria | Waffenstillstandsabkommen für Äthiopien
Ministan hulda da kasa da kasa na Afirka ta Kudu Naledi Pandor, Redwan Hussien Rameto, wakilin gwamnatin Habasha, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, wakilin kungiyar Tarayyar Afirka na kahon Afirka kuma tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, Getachew Reda, wakilin Kungiyar TPLF da kuma tsohon mataimakin shugaban kasar AfIRka ta Kudu Phumzile Mlambo-Ngcuka, sun dauki hoton bayan da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, biyo bayan shawarwarin da kungiyar tarayyar AfIRka ta jagoranta, na warware rikici a kasar Habasha, a ofishin ma'aikatar hulda da kasashen duniya da hadin gwiwar kasa da kasa (DIRCO)Hoto: PHILL MAGAKOE/AFP

Firaminista Abiy Ahmed na kasar ta Habasha ya bukaci masana su taimaka wajen ganin an samu zaman lafiya mai dorewa. Ita kanta hukumar sasantawa ta kasar ta ce tuni shiri ya yi nisa kan tabbatar da ganin an dinke barakar da aka samu sakamakon yakin basasan. Dr. Yonas Adaye ke zama hukumar tattaunawa ta kasar: "Ina tsammanin akwai lokaci da yanayin yaki kana kawai lokaci da yanayin zaman lafiya kamar yadda masu iya magana cewa. Yanzu lokaci ne na zaman lafiya, muna aiki kan tabbatar da taswirar zaman lafiya. Duk za mu je ganawa da mutanen yankin Tigray. Muna kuma ganin irin ci-gaban da ake samu. Idan wannan ci-gaban ya karfafa za mu samu damar ida garin Mekelle lokacin."

Martanin jama'ar kasar a game da shirin zaman lafiyar

Pretoria | Waffenstillstandsabkommen für Äthiopien
Jagoran masu shiga tsakani na gwamnatin Habasha, Redwan Hussein,a hannun hagu, na gaisawa da babban mai shiga tsakani na yankin Tigray Getachew Reda, yayin da tsohon shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta da ke sanye da farar riga yake tsaye tsakaninsu a tattaunawar zaman lafiya da aka yi a birnin Pretoria, na Afirka ta Kudu.Hoto: Themba Hadebe/AP/picture alliance

Ga sauran 'yan kasar Habasha abin da suke bukata shi ne zaman lafiya kamar yadda Adene Berhanu mazauniyar birnin Addis Ababa da ke cewa lokaci ya yi na samun zaman lafiya: "Lokaci ne na samun sabon gwarzo mu dade muna samun wadanda ake girmamawa saboda yaki. Muna son sabon gwarzo wanda yake imani da tattaunawa. Duk bangarorin ya dace su hau teburin tattaunawa. Mata da yara rikicin ya fi shafa, lokacin ya yi na kawo karshen haka. Mun yi imanin a karni na 21 komai za a iya tattaunawa a kai." Mutane da dama sun yi maraba da shirin zaman lafiya tsakanin gwamnatin kasra ta Habasha da mayakan yankin Tigray, abin da suke gani zai iya kawo karshen takun saka tsakanin bangarorin biyU.