1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen duniya sun soki gwajin makaman Koriya

Abdoulaye Mamane Amadou
August 28, 2019

Kasashen Jamus da Faransa da Birtaniya sun yi kakkausar suka ga matakin Koriya ta Arewa na ci gaba da yin gwaje-gwajen makaman masu cin dogon zango abin da ya sabawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/3Obes
Nordkorea | Raketentest
Hoto: picture-alliance/dpa/AP Photo/KCNA/Korea News Service

Manyan kasashen na nahiyar Turai da ke zaman mambobi a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, sun nunar da cewa akwai bukatar daukar muhimman matakai domin kwance damarar da Koriya ta Arewan ta daura kan batun makaman nukiliya.

Bayanan kasashen uku dai na zauwa ne bayan wata ganawa ta musamman da suka yi wadda ta mayar da hankali kacokam kan matsalar gwajin makaman da Koriyan ke ci gaba da yi. 

Kasashen uku sun kuma yi kira ga hukumomin Koriya ta Arewan da su sake bude tattaunawa tsakaninsu da Amirka domin kawo karshen cece-ku-ce.