1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi watsi da takardun takarar dan tsohon shugaban Libiya

Suleiman Babayo ZMA
November 25, 2021

Hukumar zaben kasar Libiya ta bayyana soke takardun da Seif al-Islam Gaddafi dan tsohon Shugaba Marigayi Moammar Gaddafi domin takara a zaben shugaban kasar da ke tafe.

https://p.dw.com/p/43Rd6
Lybien Saif al-Islam Gaddafi, Sohn des libyschen Führers Muammar Gaddafi
Hoto: Mast Irham/dpa/picture alliance

A wannan Laraba da ta gabata hukumar zaben kasar Libiya ta soke takarar Seif al-Islam Gaddafi dan tsohon shugaban kasar Marigayi Moammar Gaddafi, daga cikin 'yan takara da ke neman shugabancin kasar a zaben da aka tsara na watan gobe na Disamba.

Hukumar zaben ta ce ta dauki wannan mataki saboda ya fusakanci hukuncin da aka daure shi a kasar. A shekara ta 2015 wata kotu da ke birnin Tripoli fadar gwamnatin kasar ta yanke hukuncin kisa ga Seif al-Islam Gaddafi saboda amfani da karfi kan masu zanga-zangar juyin-juya hali na shekara ta 2011 lamarin da ya kawo karshen gwamnatin mahaifinsa Marigayi Moammar Gaddafi ta fiye da shekaru 40. Sai dai an yi masa ahuwa a shekara ta 2017, amma har yanzu kotun duniya mai hukunta manyan laifuka yaki tana neman Seif al-Islam Gaddafi ruwa a jallo.

An tsara zaben shugaban kasar zagaye na farko ranar 24 ga watan gobe na Disamba a kasar ta Libiya da ke yankin arewacin Afirka, sakamakon kwarya-kwaryar zaman lafiya bayan kulla yarjejeniya tsakanin kungiyoyin masu hamayya da juna.