1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sanar da lada kan attajirin Tanzaniya

October 15, 2018

A kasar Tanzaniya za a bayar da miliyoyin daloli ga duk wanda ya bayar da bayanai kan attajirin nan da wasu suka sace a makon jiya.

https://p.dw.com/p/36Zw8
Tansania Mohammed Dewji, Geschäftsmann
Hoto: Getty Images/AFP/K. Said

Iyayen matashin attajirin nan da ya fi kowa kudi a gabashin Afirka Mohammed Dewji da aka sace a makon jiya, sun ce za su bayar da ladar kusan dala miliyan 450, ga duk wanda ya tsegunta musu ko kuma jami'an tsaro wajen da dan nasu yake.

Shi dai Mohammed Dewji an yi awon gaba da shi a ranar Alhamis da ta gabata, inda iyayen nasa ke cewa a wannan Litinin, za su bayar da makudan kudaden tare da boye sunan duk wanda ya sanar da su ko jami'an tsaron.

'Yan sanda a birnin Dar es Salam, sun kama mutum 20 tare kuma nuna cewa suna ci gaba da bincike, kuma shugabansu a yankin Lazzaro Mambosasa, ya yi wa DW karin bayani.

'Muna ci gaba da bincike don gano inda Mohammed Dewji yake. Daga bayanan da muke tattarawa, mun gano cewa Mohammed Dewji, bai wuce kwaryar Dar es Salam ba, kuma burin wadanda ke rike da shi, bai wuce batun kudin fansa ba ne'