An samu Rubiales da laifin sumbatar 'yar wasa
February 20, 2025Talla
Kotun ta umarci Rubiales ya biya tarar sama da Yuro 10,000. An dai shafe tsawon lokacin ana ta kai kawo kan shari'ar da ya haifar da zazzafar muhawara a duniyar wasanni, matakin ya tilasta Rubiales yin murabus a matsayin shugaban hukumar kwallon kafa a Spain.
Masu gabatar da kara sun nemi kotu ta daure Rubiales mai shekaru 47 tsawon shekara biyu da rabi, sai dai tsohon dan wasan ya kafe kan cewa bi ta da kulli ne. Amma har yanzu akwai sauran mutane uku da ke jiran shari'a kan zargin tilasta 'yar wasan da karyata sumbatar dole.