1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu cikas a ƙoƙarin warware rikicin Siriya

January 28, 2012

Ƙungiyar Larabawa ta ce ayarin da ta tura Siriya ta gaza cimma manufar da ta sanya a gaba na gano bakin zaren warware rikicin ƙasar.

https://p.dw.com/p/13sTg
The empty chair of the Syrian delegate is seen during the Arab foreign ministers meeting at the Arab League headquarters in Cairo January 22, 2012. An Arab League committee on Syria will ask Arab foreign ministers on Sunday to extend a monitoring mission in the country by one month, sources attending the committee meeting said. REUTERS/Suhaib Salem (EGYPT - Tags: CIVIL UNREST POLITICS TPX IMAGES OF THE DAY CONFLICT)
Zaman taron ƙungiyar ƙasashen LarabawaHoto: Reuters

A wannan Asabar ce ƙungiyar ƙasashen Larabawa ta sanar da cewar tana duba yiwuwar kawo ƙarshen aikin tawagar da ta tura zuwa ƙasar Siriya domin sanya ido akan yadda lamura ke tafiya a cikin ƙasar, sakamakon irin matakan da hukumomin ƙasar ta Siriya ke ɗauka akan masu boren nuna adawa da gwamnati. A cikin wata sanarwar da wani jami'in ƙungiyar ya fitar, ya ce a cikin makon dake kamawa ne ministocin kula da harkokin wajen ƙasashen ƙungiyar za su gudanar da taro da nufin tattauna ko ya dace su janye tawagar sanya idon da suka tura zuwa ƙasar ta Siriya.

A halin da ake ciki kuma, ƙungiyar ƙasashen yankin tekun Fasha tare da ƙasar Turkiyya, waɗanda ke jagorantar sukar da ƙasashen yankin ke yi game irin matakan gallazawar da gwamnatin Siriya ke ɗauka akan masu zanga zangar nuna adawa da ita kuwa, sun buƙaci mahukunta a birnin Damascus na ƙasar ta Siriya da su amince da shirin da ƙungiyar ƙasashen Larabawar ta gabatar da nufin kawo ƙarshen zubda jini a cikin ƙasar - ba tare da wani ɓata lokaci ba.

A ƙarƙashin shirin dai, ƙungiyar Larabawar ta buƙaci shugaba Bashar al-Assad ya sauka daga mulki, tare da miƙa ragamar shugabanci ga mataimakin sa, kana da samar da wata sabuwar gwamnatin haɗin kan ƙasa a cikin tsukin watanni biyu, amma kuma mahukuntan na Siriya sun yi watsi da wannan shawarar.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal