1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sami Abu Walaa da alaka da IS

February 24, 2021

Bayan samunsa da alaka da kungiyar IS kotu a birnin Celle na Jamus ta yanke wa Abu Walaa hukuncin zaman gidan maza na shekaru goma da rabi.

https://p.dw.com/p/3pnqR
IS-Terrorprozess in Celle Oberlandesgericht
Hoto: Julian Stratenschulte/dpa/picture alliance

Wata kotu da ke birnin Celle a arewacin Jamus ta sami Abdulaziz Abdullah wanda aka fi sani Abu Walaa da laifin zama mamba da kuma tallafawa kungiyar IS.

Limamin masallacin da tuni aka zargi masallatan da tsatsauran ra'ayi, ya kasance wakilin kungiyar ta IS a kasar wanda kuma ya ke yaudarar matasa tare da sakasu cikin kungiyar.

Bayan kotun ta same shi da laifi ta kuma yanke masa hukuncin shekaru goma da rabi a gidan kasu.