1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake shiga wani sabon mawuyacin hali a ƙasar Masar

November 21, 2011

Bayan da aka shafe ƙarshen wannan makon ana bata kashi a dandalin Tahrir dake birnin Alƙahira, da safiyar wannan litinin an cigaba da zama cikin wani yanayi na tashin hankali

https://p.dw.com/p/13EKY
Arangama tsakanin masu bore da 'yan sanda a dandalin TahrirHoto: dapd

Kawo yanzu ba'a san adadin waɗanda suka rasu sakamakon juyin juya halin da ya kifar da mulkin tsohon shugaba Hosni Mubarak a dandalin ba, to sai dai masu boren a wannan karon sun bukaci gwamnatin riƙon ƙwaryar sojin ƙasar da ta gaggauta wajen mika wa fararen hula iko, wanda ta amsa a watan Fabrairun da ya gabata. Ana sa ran gudanar da zaɓen 'yan majalisar dokoki a mako mai zuwa amma har yanzu ba'a sa ranar zaɓen shugaban ƙasa ba.

Fiye da mutane goma suka hallaka a Masar a tarzomar da aka yi a ƙarshen makon da ya gabata. yawancinsu sakamakon harbin bindiga, wasu kuma sakamakon duka ko kuma harsasan roba, a yayin da adadin waɗanda suka ji rauni kuma ya shiga dubbai. Haka nan kuma labarin bai canza ba a sauran manyan biranen ƙasar. A dandalin Tahrir da ke tsakiyar birnin Alƙahira, an ɗan sami daidaituwa to sai dai a kan tituna, masu boren na ci-gaba da daga da jami'an tsaro.

Unruhen in Kairo Ägypten Dossierbild 3
Masu bore a dandalin Tahrir ranar lahadi da ta shigeHoto: dapd

Domin shawo kan wannan rikicin, tun a ranar asabar jami'an tsaro sun yi ƙoƙarin su kori wasu tsirarun masu boren da suka kafa tantunansu a dandalin Tahrir, nan da nan sai suka sami goyon-bayan dubban mutane daga duk sassan al'ummar daban-daban kama daga masu tsattsauran ra'ayin addini da na 'yan ba ruwan mu da addini. Dukkansu kuma suna kira da a kawo ƙarshen mulkin gwamnatin riƙon ƙwaryar sojin.

Daga farkon wannan shekarar bayan da matasa suka shafe makonni suna zanga-zanga a dandalin Tahrir, aka hamɓarar da mulkin kama karya na tsohon shugaba Hosni Mubarak, sanan sojojin suka karɓi iko. Kuma yanzu wannan ikon ne suke so su cigaba da riƙewa. A kwanan nan ne ya bayyana cewa jami'an sojin na so sabon kundin tsarin mulki ya ba su cikakken iko akan al'amuran ƙasar. Haka nan kuma a ba su damar amincewa da kuma aiwatar da kasafin kuɗin ƙasar. Waɗannan abubuwan ne masu boren ke adawa da su, domin a cewarsu ba demokraɗiyya ba ne a ce sojoji ne ke jagorantar alumma, ya kamata alumma ce zata jagoranci sojoji a matsayin wani ɓangare nata.

Zanga-zangar ta ran asabar ta bazu, inda masu boren suka yi ƙoƙarin kai hari kan hukumar cikin gida. 'Yan sanda suka tsare tituna, haka nan kuma aka yi ta bata kashi da duwatsu daga ɓangaren masu boren da kuma harsasan roba da barkonon tsohuwa daga ɓangaren 'yan sanda.

Unruhen in Kairo Ägypten
'Yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa domin fatattakar masu bore a dandalin TahrirHoto: dapd

Ran lahadi da rana, bayan masu boren sun yi sao'i 30 suna wannan bata kashin sun koma sun zauna a dandalin Tahrir, inda 'yan sanda suka sake diran musu suna harba harsasan roba da barkonon tsofuwa, cikin firgici masu boren sun tsere amma ba da daɗewa ba suka sake komawa a dubunninsu suna kuma sake faɗa da ƙwaƙƙwarar murya cewa wa'adin sojin ya cika.

Da yawa daga cikin masu boren na so a ɗage zaɓen majalisar dokokin da za'a gudanar nan da mako guda, amma ko a ranar lahadin gwamnatin riƙon ƙwaryar ta sake ba da sanarwar cewa za'a gudanar da zaɓen kamar yadda ta shirya.

Mawallafi: Björn Blaschke/Pinaɗo Abdu

Edita: Ahmad Tijani Lawal