1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sace dalibai a Najeriya

March 12, 2021

'Yan bindiga a Najeriya, sun yi awon gaba da daliban wata makaranta ta koyon dabarun noma da kula da gandun daji a jihar Kaduna da ke a arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/3qXsM
Nigeria Viehdiebstähle in ländlichen Regionen
Hoto: DW/Katrin Gänsler

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin tarayyar Najeriya ta tabbatar da sace dalibain makarantar koyon aikin gandun daji da yan bindiga suka yi a daren jiya. Wannan dai shi ne karo na hudu da ake sace dalibai a yankin Arewacin Najeriya tun daga watan Disemba.

Kwamishinan tsaron jihar Samuel Aruwan shi ne ya tabbatar da afkuwar lamarin, sai dai bai bada kiyasin yawan daliban da aka sace ba, amma dai wata majiya ta ce kimanin dalibai 30 ne yan bindigar suka yi awon gaba dasu.

Wani dalibi a makarantar da ya shaida faruwar lamarin Sani Danjuma ya ce mafi yawancin daliban da aka sace yan mata ne.