1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake kama Bobi Wine

March 15, 2021

A ranar Litinin ce dai aka kama jagoran adawar kasar Yuganda Bobi Wine bayan ya bi sahun masu zanga-zangar lumana.

https://p.dw.com/p/3qeZQ
Uganda Festnahme Robert Kyagulanyi aka Bobi Wine
Hoto: Abubaker Lubowa/REUTERS

Jawabin da aka wallafa a shafin offishinsa na twitter na nuna cewa Bobi Wine ya  jagoranci ‘yan majalisar da sauran shugabanni don nuna adawa ga garkuwa da azabtarwa da kuma kisan magoya bayansa a birnin Kampala.

Rahotannin dai na nuna cewa mahukuntan Yaganda na zargin Wine da yunkurin kawo karshen gwamnatin shugaba Yoweri Museveni ta hanyar zanga-zanga.Tun dai a ranar 10 ga wannan Maris ne dai Bobi Wine ya ce kwanaki 70 kenan da hukumomi a kasar suka kame tawagar masu gangamin goya masa baya a Kalangala.

Jagoran adawan dai ya kasance a tsare a gida a watan Janairun da ya gabata yayin da ya ke kalubalantar sakamakon zaben inda daga baya wata kotu a kasar ta yanke hukunci dangane da kamen nasa.