1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake gangami kan Shugaba Barrow

January 13, 2020

Wasu 'yan kasar Gambiya sun sake fitowa inda suka yi kira ga Shugaba Adama Barrow ya mulki kasar na shekaru biyar. Shi dai shugaban ya yi alkawarin mulkin shekaru uku ne.

https://p.dw.com/p/3W62v
Gambia Protest gegen Präsident Adama Barrow, Rücktrittsforderung
Hoto: DW/O. Wally

Dubban 'yan kasar Gambiya ne suka mamaye manyan hanyoyin Banjul, inda suke ta kiraye-kirayen Shugaba Adama Barrow da ya yi mulkin shekaru biyar, maimakon uku da ya alkawarta a shekara ta 2016.

Sabon macin Gambiyawan ya zo ne bayan wani da wasu 'yan kasar suka yi cikin watan Disamba, inda su kuwa suke bukatar shugaban da kada ya wuce shekarun uku, da ya debar wa kansa.

Shi dai Shugaba Adama Barrow, ya sanya hannu kan yarjejeniyar cewar zai kasance ne shugaba da zai mika mulki ga wata sabuwar gwamnati, bayan kawo karshen shugabancin tsohon Shugaba Yahya Jammeh.

A share guda kuwa tsohon Shugaba Jammeh, wanda a halin yanzu ke zaman hijira a kasar Equatorial Guinea, ya nuna bukatar a kyale shi da ya koma gida.

Tsawon shekaru 22 ne dai tsohon shugaban ya mulki Gambiya, inda ya sauka bayan matsin lamba daga kasashen duniya.