1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake dawo da kullen corona a Jamus

October 28, 2020

Hukumomin kasar Jamus sun sake dawo da kwarya-kwaryar kullen wata guda don hana yaduwar corona, inda aka ware kudade domin ceto kamfanonin da za su tafka asara.

https://p.dw.com/p/3kZ7I
Berlin Kanzlerin Merkel PK zu Corona-Maßnahmen
Hoto: Fabrizio Bensch/Pool/REUTERS

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da gwamnonin jihohin kasar, sun amince da amfani da kadaden da suka kai Euro biliyan 10 domin bai wa kamfanonin da za a tilasta wa rufe harkokinsu sakamakon sabbin matakan kulle da aka tsara dauka saboda hana yaduwar cutar corona a kasar.

Kanana da matsakaitan kamfanoni za su samu 75% na asarar da za su iya tafkawa cikin watan Nuwamba, yayin da manyan kamfanonin Jamus din za su sami 70%.

Hukumomin na Jamus sun ce za a rufe wuraren al'adu da na shakatawa da gidajen abinci da shagunan barasa, matakin da zai fara aiki a ranar Litinin da ke tafe.

Wasu shaguna musamman na bukatun yau da kullum za su ci gaba da kasancewa a bude, sai dai karkashin tsauraran matakan tazara tsakanin jama'a.

Su ma makarantu an amince da ci gaba da koyo da koyarwa a cikinsu, sai dai za a kara matakan tsaftace jiki lokaci zuwa lokaci.

Shagunan kwalliya da zaurukan tausa za su kansace a garkame tsawon makonni hudun da ke tafe, a cewar mahukuntan kamar yadda su ma wasannin Lig-Lig na Jamus wato Bundesliga, za su kasance babu 'yan kallo.