1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi garkuwa da Bajamushe limamin coci a Mali

Abdul-raheem Hassan
November 21, 2022

An gano motar Hans-Joachim Lohre a Bamako, babban birnin kasar Mali kusa da makarantar da yake koyarwa. Mutumin wanda asalin dan kasar Jamus ya kai shekaru 30 yana aiki a Mali.

https://p.dw.com/p/4JqBr
Sojan Barkhane a Mali
Hoto: Philippe De Poulpiquet/MAXPPP/dpa/picture alliance

Wasu da ake zargin masu kaifin kishin addini sun yi garkuwa da wani limamin coci dan kasar Jamus a Bamako babban birnin kasar Mali, Wannan dai shi ne karon farko cikin shekaru 10 da aka sace wani dan kasar yammacin duniya a Mali.

Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin yin garkuwa da limamin cocin, wanda ya shafe fiye da shekaru 30 a Mali, sai dai tuni aka dora zargi kan kungiyar IS mai tarihin garkuwa da 'yan kasashen waje don samun kudin fansa.