1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rushe majalisar dokokin Masar.

February 13, 2011

Sojoji sun fara ɗaukar matakan biyan buƙatun masu zanga zanga a Masar tare da rushe majalisar dokoki da kuma jingine kundin tsarin mulkin ƙasar

https://p.dw.com/p/10Gf9
Janar Mohsen el-Fangari na majalisar koli ta soji a Masar.Hoto: AP

Sabbin shugabannin mulkin soji a Masar sun sanar da rushe majalisar dokoki da kuma jingine kundin tsarin mulkin ƙasar , kwanaki biyu bayan murabus ɗin shugaba Hosni Mubarak. A cikin wata sanarwa Majalisar ƙolin sojin ta ce za ta ci-gaba da gudanar da al'amuran ƙasa har izuwa lokacin da za'a gudanar da zaɓen sabbin 'yan majalisun dokoki. A yau gwamnatin riƙon ƙwaryar ta gudanar da taronta na farko inda ta baiyana cewa babban abinda ke gabanta a yanzu shine maido da doka da oda da kuma sauƙaƙa harkokin rayuwar jama'a. Firaministan ƙasar Ahmed Shafiq ya ce ba zai yi saurin naɗa muƙaman Ministoci ba yana mai cewa zai yanke hukunci ne idan ya sami tabbacin amanna na mutanen da za'a naɗa.

" Yace babban abinda ya fi damun mu a yanzu shine batun sha'anin tsaro. Muna buƙatar ganin al'umar Masar sun dawo cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Tun bayan fara zanga zanga al'amura suka sauya, sai dai muna fata sannu a hankali komai zai daidaita. Za mu tabbatar da ganin al'umar Masar sun cigaba da harkokin rayuwarsu kamar yadda suka saba tare da samar musu muhimman buƙatun rayuwa kamar harkokin lafiya da sauƙaƙa tsadar abinci".

Mwallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Ahmed Tijani Lawal