1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Jagoran adawar Rasha ya sha guba

August 20, 2020

Ana ci gaba da nuna damuwa kan lafiyar jagoran adawar kasar Rasha Alexei Navalny bayan an ruga da shi zuwa asibiti a safiyar Alhamis din nan.

https://p.dw.com/p/3hFcQ
Alexej Navalny
Hoto: Imago Images/Itar-Tass/S. Fadeichev

Rahotanni daga asibitin da aka kwantar da shi a birnin Omsk na kasar Rasha sun ce kawo yanzu ana zargin jagoran adawar na Rasha ya hadiyi guba ne, a wani lamari da ke da matukar daure kai. 


Bayanan da DW ta samu na nuni cewa Alexei Navalny ya shiga cikin yanayin rai-kwakwai-mutu-kwakwai, inda aka ce an sanya masa na'urar taimaka wa numfashi domin ya samu ya murmure. Gwamnatin Rasha dai ba da jimawa ba ta sanar da cewa tana yi wa jagoran adawar fatan alheri, yayin da kungiyar tarayyar Turai ta EU ta ce ta kadu matuka da wannan labari.