1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Rufe bankunan ajiyar dakarun RSF

Binta Aliyu Zurmi
May 16, 2023

Rahotanni daga Sudan na cewar shugaban sojin gwamnati janar Abdel Fatah al Burhan ya bada umurnin rufe bankunan ajiyar kudin rundunar sa kai ta RSF.

https://p.dw.com/p/4ROEv
Sudan Khartoum | Zeremonie zur Unterzeichnung eines Rahmenabkommens zwischen Militärherrschern und Zivilmächten
Hoto: El Tayeb Siddig/REUTERS

A cewar kafar yada labarun kasar ta SUNA, wannan sabon hukuncin zai shafi dukacin 'yan rundunar RSF da ke da bankuna a kasar gami da kamfanon i mallakinsu.

A karshen makon da ya gabata ne janar Burhan ya sauya gwamnan babban bankin kasar, ya zuwa yanzu babu tabbacin yadda wannan sabon hukuncin zai shafi rundunar da ma yadda take ci gaba da fito na fito da sojojin gwamnati.

Tun a tsakiyar watan Apirilu ne fada ya barke tsakanin sojojin gwamnati da ke karkashin Abdel Fatah al Burhan da kuma ta rundunar sa kai karkashin Mohamad Hamdan Dagolo.

Majalisar Dinkin Duniya da manyan kasashen duniya na ci gaba da kokarin kawo karshen wannan rikicin da bangarorin masu gaba da juna ke ci gaba da kaura fada.