1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Arangamar Falasdinawa da 'yan sanda a Kudus

Abdoulaye Mamane Amadou
May 8, 2021

Fiye da mutane 180 sun jikkata ciki har da jami'an 'yan sanda a harabar masallacin Kudus a Isra'ila, biyo bayan barkewar rikici tsakanin Filastinawa da jami'an tsaro.

https://p.dw.com/p/3t8KC
Israel | Ausschreitungen in Jerusalem
Hoto: Ahmad Gharabli/AFP/Getty Images

'Yan sanda sun yi amfani da kulake da harsashen roba wajen tarwatsa masu boren da suka fara nuna adawa kan matakin Isra'ila na korar Falastina, jim kadan bayan tashi daga sallar Juama'a, a daidai lokacin da Musulmi ke kara tsananta ibadunsu a kwanakin 10 karshe na wannan wata.

Tuni dai kungiyar Hamas mai iko da zirin Gaza ta yi kira ga Filasdinwa da su ci gaba da jajricewa tare da yin tsayuwar ibadunsu na daren 27 ga watan Ramadan a harabar masallacin a wannan Asabar.

Sai dai duk da yake rahotanni sun ce kura ta lafa, kasashen duniya da dama ciki har da Amirka da Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da nuna fargaba kan abinda ka iya faruwa biyo bayan rikicin.