1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rantsar da sabon Fremiyan Girka

June 20, 2012

Sabon Fremiyan Girka Antonis Samaras ya kama aiki a matsayin sabon shugaban gwamnatin ƙasar bayan da jam'iyarsa mai ra'ayin rikau ta lashe zaɓe.

https://p.dw.com/p/15Ihu
Newly appointed Greek Prime Minister Antonis Samaras (R) is sworn in as President Karolos Papoulias (C) attends the ceremony at the presidential palace in Athens June 20, 2012. Samaras pledged to pull his debt-stricken country back from the brink of bankruptcy on Wednesday in his first comments after being sworn in. REUTERS/Yorgos Karahalis (GREECE - Tags: POLITICS BUSINESS TPX IMAGES OF THE DAY)
Hoto: Reuters

Antonis Samaras ya rantse a matsayin sabon fremiyan ƙasar Girka bayan da jam'iyarsa mai ra'ayin rikau ta New Demokratie (Wato ND) ta lashe zaɓen da a ka gudanar a ƙarshen makon jiya. Shi dai Antonis Samaras ɗan shekaru 61 a duniya, ya samu goyon bayan manyan jam'iyun siyasar ƙasar da suka haɗa da masu ra'ayin gurguzu, mai kujeru 179 daga cikin yawan kujeru 300 a majalisar dokoki da kuma jam'iyar masu sasauci.

Ana kuma sa ran a cikin makon nan ne zai kafa sabuwar gwamnatinsa. Masana al'amuran ƙasar na ganin sabon shugaban gwamnatin nada babban ƙalubale a gabansa bisa ga yadda ƙasashen tarayyyar Turai ke ɗari-ɗari da ƙasar a kan batun tattalin arzikinta.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Zainab Mohammed Abubakar