1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nesanta siyasa da zuwan Jonathan Borno

Ahmed SalisuJanuary 16, 2015

Kakakin shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce ziyarar da shugaban ya kai Borno a jiya ba ta da nasaba da zawarci kuri'un al'ummar kasar gabannin zaben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/1ELT7
Nigeria Goodluck Jonathan
Hoto: AFP/Getty Images

Gwamnatin Najeriya ta ce zuwan da shugaban kasar Goodluck Jonathan ya yi jihar Borno a jiya Alhamis don ziyarar 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu da kuma sojin da ke fafutuka wajen dakile tada kayar bayan 'yan kungiyar ba ta da nasaba da siyasa sabanin yadda 'yan siyasa da sauran al'ummar kasar ke fadi.

Kakakin shugaban Najeriyar Reuben Abbati ne ya bayyana hakan a jiya ga manema labarai ciki kuwa har da wakilin DW da ke Abuja Ubale Musa, inda ya ke cewar ziyarar wani mataki na nuna hali na sanin ya kamata wajen jagorantar al'ummar kasar.

Ziyarar ta Jonathan a Borno dai ita ce irinta ta farko a jihar tun bayan da aka sace 'yan matan nan na makarantar sakandaren gwamnati ta Chibok su sama da 200 da Boko Haram suka sace.