1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An dakatar da Sudan daga AU

Abdoulaye Mamane Amadou
October 27, 2021

Kwanaki bayan hambarar da gwamnatin farar hula a Sudan, Kungiyar Tarayyar Afirka AU ta dakatar da kasar daga cikin jerin membobinta har sai an dawo da gwamnatin da sojoji suka rusa.

https://p.dw.com/p/42FJ6
Putsch im Sudan General Abdel Fattah al-Burhan
Hoto: Marwan Ali/dpa/picture alliance

A cikin wata sanarwar da ta fitar a wanna Laraba, AU ta yi kakkausar suka ga matakin kwace mulki da karfin bindiga da soji suka yi a farkon wannan makon, haka da matakin rusa majalisar koli ta rikon kwarya karkashin jagorancin farar hula da sojojin suka yi, tana mai cewa ba za ta sabu ba.

Sai dai kungiyar ta kuma yaba da sakin hambararen firaminista Abdallah Hamdock, tare da kira da a sallami ragowar ministocin gwamnatin da ke rike a hannun sojin.

Wannan dai shi ne karo na biyu da AU ke dakatar da Sudan daga cikin jerin membobinta, tun bayan wani makamacinsa a 2019 biyo bayan hambarar da mulkin Omar Albashir.