1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ASEAN ta mayar da Myanmar saniyar ware

Ramatu Garba Baba MNA
October 16, 2021

A karon farko Myanmar ba za ta halarci taron koli na kungiyar kasashen Kudu maso gabashin Asiya ba don nuna adawa ga sojojin da suka kwace mulki da karfin tuwo.

https://p.dw.com/p/41log
TABLEAU | Indonesien Jakarta | ASEAN-Gipfel zu Myanmar | Joko Widodo, Präsident Indonesien
Hoto: Laily Rachev/Indonesian Presidential Palace/REUTERS

Shugabannin kungiyar kasashen Kudu maso gabashin Asiya ko ASEAN, sun ki mika goron gayyata ga sojojin da suka karbe madafun ikon kasar Myanmar daga halartar taron kungiyar da ke tafe. A wani taron gaggawa da shugabannin suka gudanar a ranar Juma'a, suka dauki matakin kin damawa da gwamnatin da ake wa kallon haramtacciya a sakamakon hambarar da gwamnatin Aung San Suu Kyi.

A martanin da gwamnatin Myanmar din ta mayar, ta ce, kungiyar ta dauki matakin ne bisa tursasawa daga kasashen Turai da Amirka.

Wannan shi ne karon farko da kungiyar ke fitowa karara ta nuna rashin amincewa da gwamnatin da ke rike da ikon Myanmar. Kasar da ke fama da rikicin kabilanci da addini, ta kuma fada cikin tashe-tashen hankula bayan hambarar da gwamnatin San Suu Kyi. Fararen hula sama da dubu daya suka rasa rayukansu a hannun jami'an sojin da suka kwace iko da karfin tuwo.