1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kwantar da Shugaba Trump a asibiti

October 3, 2020

An kwantar da Shugaba Donald Trump na Amirka a asibiti bayan kamuwar da ya yi da cutar corona. Wasu majiyoyi daga mashawartan Mr. Trump, sun ce akwai dalilai da za su a damu.

https://p.dw.com/p/3jNlC
Washington | Trump Abflug Militärkrankenhaus
Hoto: Saul Loeb/AFP/Getty Images

Rahotannin da ke fitowa daga Amirka, na cewa ana yi wa Shugaba Donald Trump jinya da maganin nan na remdesivir, bayan tabbatar da kamuwarsa da kwayar cutar nan ta corona tare da mai dakinsa Melania a jiya Juma'a.

A halin yanzu dai shugaban na Amirka na kwance ne a asibiti, kuma likitansa ya ce babu wani abin damuwa game da halin da Mr. Trump ke ciki.

Sai dai tun da farko wasu rahotannin sun ce shugaban ya fara nuna wasu alamun tsananin cutar, wadanda suka hada da toshewar hanci da kuma kaikayi na makogwaro.

Wasu kwararru na cewa babu tabbas a kan ingancin maganin remdesivir, maganin da wani babban kamfanin harhada magunan nan na Gilead Scinces ya samar don maganin cutar Ebola.

Sai dai a daya hannu  wasu masana na cewa maganin na iya yin tasiri kan kwayar cutar corona.