1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus: An kwace lasisin malamin Musulunci

June 26, 2021

A Jamus wata gidauniya da ake kira Stiftung Sunnitischer Schulrat, da Jamusanci,  ta kwace  lasisin zama malamin addinin Islama daga hannun Abdel-Hakim Ourghi da ke zama malamin Islama a jam'iar birnin Freiburg.

https://p.dw.com/p/3vbIy
Islamreformer Abdel-Hakim Ourgh
Hoto: Rolf Haid/picture alliance

Kawo yanzu dai gidauniyar da ke da ikon tantance maluman addinin Islama a jihar Baden-Württemberg da ke kudu maso gabashin Jamus ba ta zayyana dalilanta na karbe shaidar malumtar daga hannun malamin ba. Sai dai wata Bajamushiya mai bincike a kan addinin Musulumci Susanne Schröter ta yi zargin gidauniyar ta kwace wa malamin lasisi ne saboda sassaucin da yake da shi a cikin fatawowinsa na Musulumci wadanda ke cin karo da fatawowin sauran malaman da ake wa kallon masu tsattsauran ra'ayi ne. 
Malam Abdel-Hakim dai ya wallafa wani littafi a baya wanda ya haddasa cece-kuce a tsakanin masana Musulumci a Jamus, inda a cikin littafin ya nuna cewa mata Musulmai ba sa bukatar sanya hijabi idan za su fita waje ko za su shiga bainar jama'a. 

A hirarsa da jaridar Jamus ta Die Welt, malamin ya yi zargin cewa an kwace masa lasisin malumtarsa ta Musulumci ne saboda yadda yake tallata Musulumci mai sauki ga jama'a. A yanzu dai malamin na da ikon shigar da kara don bukatar dawo masa da lasisin.