1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana kokarin ceto mutanen da suka makale a Indiya

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
November 24, 2023

Jami'an agaji a na fuskantar tangarda wajen aikin ceto mutane 41 da suka makale a karkashin kasa a jihar Uttarakhand da ke arewacin Indiya kwanaki 13.

https://p.dw.com/p/4ZOCT
Yadda ake aikin ceto mutanen da suka makale a Uttarakhand Hoto: AP Photo/picture alliance

Masu ayyukan ceto a kasar Indiya sun ce saura nisan mitoci 14 kacal su kai ga mutane 41 masu aikin gina hanya da suka makale a karkashin kasa kusan makonni biyu a jihar Uttarakhand mai tarin tsaunuka.

Wani babban jami'in gwamnatin kasar Bhaskar Kulbe, ya ce an yi nasarar zura wani bututu mai tsawon mita 57 a karkashin kasa.

Amma wata sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar ta ce komai na iya canzawa saboda matsalolin fasaha da ƙalubalen yankin Himalaya, da kuma abubuwan da ba a zata ba.

‘Yan uwan mutanen da abin ya shafa sun yi dandazo a wajen ramin cikin damuwa, ana kuma yin adduo’i a wurin ibadar Hindu da aka kafa a kofar shiga. Masana sun yi gargadin cewa tasirin gine-gine masu yawa a Uttarakhand, shi ke haddasa zabtarewar kasa.