1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An kunce bam na lokacin yakin duniya na biyu a Hamburg

October 13, 2024

An tilastawa dubban mazauna anguwar Sternschanze da ke birnin Hamburg na Jamus barin gadajensu bayan gano bam tun na lokacin yakin duniya na biyu a lokacin da ake gini a harabar wata makarantar firamare.

https://p.dw.com/p/4ljA5
Jamus: Kunce bam na lokacin yakin duniya na biyu a birnin Hamburg
Jamus: Kunce bam na lokacin yakin duniya na biyu a birnin HamburgHoto: Benjamin Haller/dpa/picture alliance

Hukumar jami'an kwana-kwana ta Jamus ta gudanar da gagarumin aiki na kunce wani bam tun na lokacin yakin duniya na biyu da aka gano a wata anguwa da ke birnin Hamburg a daren ranar Asabar.

An tilastawa duban mazauna anguwar da aka gano bam din barin gidajensu tare da rufe gidajen cin abinci da na raye-raye na anguwar da ake kira Sternschanze a lokacin da ake gudanar da wannan aiki mai matukar hadari. Har ila yau gano bam din ya kawo cikas ga zirga-zirgar jiragen kasa mausamman a tashar jiragen kasa ta Sternschanze wadda ke samun cunkoson jama'a a duk karshen mako.

Karin bayani: Barnar ababen fashewa a Jamus

An gano bam din a lokacin da ake aikin gini a harabar wata makarantar firamare, kuma a cikin wata sanarwa da hukumar jami'an kwana-kwana ta fidda da sanhin safiyar Lahadi ta ce an kunce bam din ba tare da an samu wata matsala ba bayan share sa'o'i kusan shida ana aiki.