An kori wani Limami mai tsattsauran ra'ayin adini a Beljiyam
July 14, 2015Talla
Shi dai wannan Limamin mai suna Shayh Alami, na a birnin Vervier ne a kasar ta Beljiyam kuma dan kasar Holland ne amma kuma tushensa dan asalin kasar Maroko. Yana da mata da kuma 'ya'ya hudu kuma yana Limancin ne a wani Masallaci na 'yan Somaliya da ke birnin na Vervier.
A jiya Litinin ne dai hukumomin da ke kula da 'yan gudun hijira na kasar ta Beljiyam suka dauki wannan kudiri na korar wannan Limami har na tsawon shekaru 10 nan gaba. Hukumomin dai sun bashi kwanaki talatin na ya bar kasar amma kuma sun ce ya na da damar daukaka kara kan wannan mataki a gaban kotu.