An kori jami'an diflomasiyar Rasha 100
March 26, 2018Talla
Kasashen Amirka da Kanada da Ukraine da kasashe 15 daga Kungiyar Tarayyar Turai sun bi sahu wajen tisa keyar jami'an diflomasiyar Rasha bisa zarginsu da zama jami'an leken asiri da ke aiki kamar jami'an diflomasiya.
Firamanistar ta Birtaniya May ta fada wa majalisar dakoki a Birtaniya cewa wannan shi ne kora mafi girman da jami'an na Rasha suka taba ganin babbar kora a tarihi:
"Na samu hadin kai daga abokanmu da kawaye daga EU da Amirka ta Arewa da mambobi na NATO da sauransu." A cewar May dai halayyar da Rasha ke nunawa babbar barazana ce ga kafatanin kasashen yammacin duniya.