1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kona ofishin jakadancin Jamus a Sudan

September 14, 2012

Masu zanga zangar adawa da fim din batanci ga addinin musulunci sun afkawa ofisoshin jakadancin Jamus da Burtaniya a birnin Khartoum. Sai 'yan sanda sun yi amfani da barkono mai sa hawaye wajen tarwatsa su.

https://p.dw.com/p/169LH
A Sudanese demonstrator burns a German flag as others shout slogans after torching the German embassy in Khartoum during a protest against a low-budget film mocking Islam on September 14, 2012. Around 5,000 protesters in the Sudanese capital angry over the amateur anti-Islam film stormed the embassies of Britain and Germany, which was torched and badly damaged. AFP PHOTO / ASHRAF SHAZLY (Photo credit should read ASHRAF SHAZLY/AFP/GettyImages)
Sudan Khartum Angriff auf deutsche BotschaftHoto: AFP/Getty Images

A kasar Sudan dubun dubatan musulmi dake zanga zangar nuna bacin rai da fim din da ya yi batanci ga addinin musulunci sun afkawa ofisoshin jakadancin Jamus dana Burtaniya a birnin Khartoum inda suka yi mummunan barna. 'Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga zangar yayin da wasu masu daga cikinsu suka dare rufin ginin wasu kuma suka tunkari gaban ginin inda suka maye gurbin tutar Jamus dana Islama.

Bugu da kari masu zanga zangar sun datse hanyoyi domin hana motar kwana kwana kashe wutar gobarar da suka cinna a ofishin jakadancin. Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle yace ma'aikatan ofishin jakadancin lafiyarsu lau suna kuma tuntubarsu kai tsaye. Ita ma ma'aikatar harkokin wajen Birtaniya wadda aka lalata ofishinta na jakadanci a Sudan ta ce tana bin lamarin dake faruwa a Khartoum sau da kafa.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Mouhamadou Awal