1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hawa teburin tataunawa a kan kogin Nilu

Binta Aliyu Zurmi
September 23, 2023

Kasashen Habasha da Masar da Sudan sun koma teburin tattaunawa a kan takaddamar nan ta gina madatsar ruwa a kogin Nilu, da ta jima tana janyo kai ruwa rana a tsakanin kasashen uku.

https://p.dw.com/p/4WjGZ
Äthiopien Renaissance-Staudamm
Hoto: Minasse Wondimu Hailu/AA/picture alliance

Wannan na zuya ne bayan da Habasha ta sanar da kammala mataki na 4 kuma na karshe na cike kogin, matakin da ya janyo martani mai zafi daga Masar da suka kira lamarin da haramtacce. Wannan ne zama na biyu a tattaunawa tsakanin kasashen 3 da ke gudana a yau din nan a birnin Addis Ababa, inda Habasha ke cewar tana fatan su cimma matsaya cikin kwanciyar hankali.

Masar da Sudan na kukan sabon aiki a madatsar ruwan ka iya kaisu ga karancin ruwa. Sai dai ko kafin yanzu, Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin nan da shekarar 2025 Masar ka iya shiga kangi na rashin ruwa da kuma wani sashi na kasar Sudan biyo bayan wannan mataki na cike madatsar ruwan Nilu.