1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe mai zanga-zanga daya a Sudan

Mouhamadou Awal Balarabe
October 25, 2022

'Yan sanda sun amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa dubban 'yan Sudan da suka yi amfani da zagayowar ranar juyin mulki wajen ci gaba da neman kafa gwamnatin farar hula a kasar.

https://p.dw.com/p/4Ifxx
Proteste im Sudan
Hoto: Marwan Ali/AP/dpa/picture alliance

An bada rahoton kashe wani mai zanga-zanga daya a boren zagayowar ranar juyin mulkin Sudan, amma ba a san yawan mutane da suka jikkata ba. Sai dai hukumomin sun toshe yanar gizo tare da amfani da borkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zanga.

Bayanai sun nunar da cewa masu zanga-zangar sun kafa shingaye don hana jami'an tsaro tinkararsu yayin da sojoji suka toshe gadoji da hanyoyin domin hana su zuwa fadar shugaban kasa. A rana mai kamar ta yau a Shekara guda da ta gabata ne, Janar Abdel Fattah al-Burhane ya saba alkawuran da ya yi shekaru biyu da suka gabata, lamarin da ya dada jefa Sudan cikin mawuyacin halin tattalin arziki.

Masu zanga-zanga 119 ne suka mutu a cikin shekara guda sakamakon fafutkar da suka yi wajen neman tabbatar da dimokuradiyya a Sudan.