1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An kashe fafaren hula a iyakar Nijar da Mali

July 30, 2021

Akalla fararen hula 19 ne aka tabbatar da salwantar su a wani sabon hari a yammacin Jamhuriyar Nijar iyaka da Mali, kamar yadda hukumomi suka sanar.

https://p.dw.com/p/3yJ4h
Mali Angriff auf das Dogon-Dorf Sobane Da
Hoto: Reuters/M. Konate

Harin ya auku ne a kauyen Deye Koukou na yankin Banibangou, inda aka yi asarar wasu mutum 14 a ranar Lahadin da ta gabata.

Akwai ma karin wasu mutum uku da suka jikkata a sabon harin da ya faru ranar Laraba.

Jimilla dai rayukan mutane 33 ne aka rasa cikin kasa da mako guda a yankin na Banibangou.

Banibangoun ta hada iyakokin kasashen uku, wato Njar da Burkina Faso da ma kasar Mali, kasashen da duk ke fama da hare-haren masu ikirarin jihadi da ke da alaka da kungiyoyi irin su Al-Qaeda da IS na kasashen Larabawa.