1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso: An hallaka fararen hula

Abdoulaye Mamane Amadou
July 18, 2022

Maharan da ake kyautata zato masu ikrarin jihadi ne sun kashe gwamman fararen hula a wani kazamin harin da suka kai a arewacin Burkina Faso iyaka da Nijar

https://p.dw.com/p/4EJRl
Benin | Fotoreportage Marco Simoncelli aus Porga
Hoto: Marco Simoncelli/DW

Wasu gwamman fararen hulla sun gamu da ajalinsu a Burkina Faso sakamakon wani harin ta'addanci a lardin Yagha mai iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Majiyar tsaro ta tabbatar wa manema labarai cewa maharan sun kuma kwashe abinci da dabbobin al'ummar yankin da suka kai wa harin na daren Lahadi.

Kamar sauran makwabtanta Mali da Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso na fuskantar hare-haren 'yan bindiga masu ikrarin jihadi, inda kawo yanzu kaso 40 cikin dari na kasar baya hannun gwamanti.