1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe Edgar Raupach a Kano

May 31, 2012

Bajumashen nan Raupach da aka yi garkuwa da shi a arewacin Najeriya ya rasa ransa lokacin da sojoji suka yi yunƙurin kuɓutar da shi a Kano.

https://p.dw.com/p/155Qo
Nigeria mit der Stadt Kano hervorgehoben --- DW-Grafik: Peter Steinmetz
Hoto: DW

Bajamushen nan da kungiyar Aqmi mai tsattsauran ra'ayin addinin musulunci ke garkuwa da shi ya gamu da ajalinsa a birnin kano, lokacin da jami'an tsaron Najeriya suka yi yunkurin kubbutar da shi a gidan da ya ke tsare. Tun da dai da sanyi safiyar wannan alhamis ne sojojin suka yi wa gidan da aka tsare Edgar Raupach kawanya bayan da suka sami sahihan bayanai game da inda aka tsugunar da shi.

Wata majiya ta soje ta bayyana cewa waɗanda suka yi garkuwa da injiniyan ɗan asalin Jamus sun harbe shi a ka kafin a yi nasarar kuɓutar da shi. Sai dai ta ce sojojin sun kashe biyar daga cikin masu tsananin kishin addinin. Tun a watan Janerun wannan shekarar da muke ciki ne, aka sace Raupach a Kano, kwanaki ƙalilan bayan hare-haren bama da ƙungiyar Boko Haram ta ɗauki alhaki. Ita Aqmi da ta yi wannan aika aika ta nemi yin musayar Edgar Raupach da wata musulma da ke tsare a Tarayyar Jamus.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar tun a watan Maris cewa ta cafke mutane biyar ciki har da dan Mauriteniya ɗaya da ke da hannu wajen sace bajamushen.

A ɗaya hannun kuma, ma'aikatar harkokin wajen Italiya ta sanar da cewa an sace wani injiniyanta a jihar Kwara ta Najeriya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal