1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala taron Majalisar Al'ummar China

March 14, 2012

Taron majalisar al'ummar ƙasar China ya kammala zamansa, inda batun tattalin arziki ya kankane ɗaukacin zaman

https://p.dw.com/p/14JB2
Top Chinese leaders, from left, Luo Gan, Wu Guanzheng, CPPCC Chairman Jia Qinglin, President Hu Jintao, Premier Wen Jiabao, Vice President Zeng Qinghong, and Li Changchun attend the Fourth Session of the Tenth National People's Congress (NPC) held at the Great Hall of the People in Beijing March 5, 2006. (AP Photo/Xinhua/Ma Zhancheng)
Tsau´ren majalisar al'ummar ChinaHoto: AP

A kammala taron shekara-shekara da majalisar al'ummar China, wanda aka yi kwanaki goma ana yi. A zahiri dai taron wakilan na jeka na yika kane, inda basa sauya wani abun da gwamnati ta tsara. Amma dai za a iya cewa taron ya baiwa wakilan sanin kaɗan daga manufofin gwamnatin ƙasar, wanda aka ɓoye wa sauran duniya.

Babban abinda taron ya maida hankali dai shine batun tattalin arzikin Chin, a jawabin da firiminyan ƙasar Wen Jiabao ya gabatar wa mahalarta taron, ya shaida musu cewa an samu koma baya kaɗan na haɓakar tattalin arziki. Hakan dai yana nufin ba za a samar da guraben aiki yi masu yawa kamar yadda ake buƙata ba. Ammma dai daga ƙarshe an tattabar da cewa tattalin arzikin ƙasar zai ci gabada kasancewa mai ƙarfi. Ko mi ya sa yanzu China ta yi hasashen samun raguwar haɓaka. Gu ZuXuewu shine daraktan cibiyar nazari ta Center for Global Study dake birnin Bonn.

FILE - In this Sept. 4, 2007 file photo, workers assemble toys at the production line of Dongguan Da Lang Wealthwise Plastic Factory in Dongguan, China A reader-submitted question about what happens to recalled Chinese-made products, is being answered as part of an Associated Press Q&A column called "Ask AP." (AP Photo/Eugene Hoshiko, File)
Ma'aikata a kasar ChinaHoto: AP

"A yanzu Gwamnatin ƙasar ta sake tsare-tsaren ta na tattalin arziki, don haka waɗannan sauye-sauye sune za su shafi haɓakar da ƙasar ke yi. Idan mutum na son samar da wasu ababen walwala, to ba lallai bane sai ya rage wuraren aikin yi"

Chinese Premier Wen Jiabao greets people upon arrival in New Delhi, India, Wednesday, Dec. 15, 2010. Wen is on a three-day visit to India as part of efforts to build trust between the rival neighbors amid lingering disputes over territory, trade and telecoms. (AP Photo/Gurinder Osan)
Firimiyan kasar China Wen JiabaoHoto: AP

Manufa dai itace ingantaccen ɗorewar tattalin arziki dake zabura. A yanayin da tattalin arzikin Amirka da ƙasashen Turai yake cikin matsala, to haka ma ya shafi fitar da haja da ƙasar China ke yi izuwa ƙasashen ƙetare, mai yiwa hakan ne ya shafi habakar tattalin arzikin ƙasar. A ra'ayin masanin siyasa Willy Lam dake Hongkong

"Kada fa a man ta da cewa habakar tattalin arziki ya samu koma baya tun shiga uku da tattalin arzikin duniya ya samu a shekara ta 2008, hakan ya sa manyan wurare da ake zuba jarin sun samu koma baya. Amma wannan bawai shine babban mafita ga ƙasar China ba, abinda zai taimaki ƙasar shine, ta yadda za ta biya buƙatun yan ƙasar ta"

Chinese paramilitary police officers march on Tiananmen Square near the Great Hall of the People as security is tightened in the area in preparation for the National People's Congress, in the Chinese capital of Beijing Friday, March 4, 2005. The annual session of the NPC begins on Saturday. (AP Photo/Greg Baker)
Rundunar sojan ChinaHoto: AP

Ɓangaren soji a ƙasar ta China dai ya samu ƙarin kason sama da kashi 11 cikin dari a bana. Ma'aikatar tsaron ƙasar an raba ta gida biyu kuma ya haɓa sosai yan shekarun nan. China tana son inganta matsayin ta a yankin Asiya, kuma tana lura da take-taken ƙasar Amirka a yankin baki ɗaya. iniji Lam

"Wannan ya shafi harkar soji. Ƙasar Amirka a dalilin rugujewar tattalin arzikinta, dole ta rage kudin da take kashewa ayyukan sojinta. Ga ƙasar China hakan wata dama ce ta inganta ƙarfin sojin ruwa da na saman ta"

Waɗannan matsaloli dai ba abune da taron wakelan zauren al'ummar ƙasar zai cimma ba, yanzu abin jira shine bayan sauya shugabancin ƙasar da za a yi a kaka'ar bana, inda Hu Jintao da Wen Jiabao za su miga ragamar mulki ga sabbin jini. Bayaga shugaba da firimiyan, akwai wasu gurabe bakwai dake da ƙarfi a tsakiyar gwamnatin China wadanda suma za a maye gurbinsu a bana. Daga nan za a ga inda ƙasar ta dosa.

Mawallafa: Haiye Cao/Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu